Connect with us

Sports

Qatar 2022: Sabbin Abubuwa 7 A Gasar Kofin Duniya

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAH 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Kwanaki biyar suka rage a soma gasar kwallon kafa ta cin Kofin Duniya a kasar Qatar, bayan shekara hudu da yin irinsa a kasar Rasha a 2018.

 

Advertisement

Ga jerin wasu abubuwa sabbi da za a gani a gasar ta bana, wadda kasashe 32 za su fafata a gaban ’yan kallo kimanin 1.2 a Doha, babban birnin kasar Qatar.

 

Advertisement

Yadda Soludo Ya Yi Wa Peter Obi Wankin Babban Bargo

1. Karon Farko A Gabas Ta Tsakiya: Wannan shi ne karon farko a tarihi da wata kasar Larabawa da ma daukacin yankin Gabas ta Tsakiya ta karbi bakuncin gasar cin Kofin Duniya.

 

Advertisement

2. Alkalan wasa mata: A karon farko mata za su yi alkalancin wasa a tarihin gasar. An nada mata uku a cikin mutum 36 da za su yi alkalancin wasannin — Matan su ne Stephanie Frappat daga kasar Faransa da Yoshimi Yamashita daga Japan sai Salima Mukansanga daga Ruwanda. Akwai kuma karin mata 69 da za su je gasar a matsayin mataimakan alkalan wasa.

 

Advertisement

3. Na farko a watan Nuwamba: Qatar 2022 shi ne gasar Kofin Duniya na farko da za a buga watan Nuwamba zuwa Disamba, sabanin na shekarun baya da aka saba yi a watan Yuni zuwa Yuli. An sauya lokacin ne domin guje wa yanayin zafin Qatar da kan kai maki 50 a ma’aunin selshos a Yuni-Yuli, zuwa Nuwamba/Disamba inda yanayin zafin ke komawa tsakanin maki 14 zuwa 31 na ma’aunin selshos.

 

Advertisement

4. Karin sauyin ’yan wasa: A karon farko kowace tawaga za ta iya yin sauyin ’yan wasa biyar a wasa guda, sabanin uku da aka saba yi a baya. Idan wasa ya shiga karin lokaci, an yarje wa kowane bangare yin sauyin dan wasa guda daya.

 

Advertisement

5. Karin ’yan wasa: An sahale wa kowacce tawaga tura ’yan wasa 26, wato karin mutum uku kan na gasar da aka yi a Rasha. Haka ma an kara yawan ’yan wasan da za su gabatar na sharar fage daga 35 zuwa 55.

 

Advertisement

6. Na’urar gano satar gida: Za a fara amfani da wannan fasaha ta zamani da za ta gano, ta dauki hoton dan wasan da ya yi ta kuma bayyana domin ’yan kallo, har a gidajensu su gane dalilin da alkalin wasa ya yanke hukunci.

 

Advertisement

7. Tsukakken wurin gasa: Za a yi gasar ne a kasar mafi kankanta da ta taba daukar nauyin gasar ta FIFA a tarihi. Dukkkanin filayen da za yi wasannin ba su da nisa da juna a birnin Doha mai fadin kilomita 50. Wasu filayen wasan za buga wasa a cikin har sau hudu a rana kuma ana hasashen samun cinkoso sakamokon halartar mutane kimanin miliyan 1.2.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Al Jazeera

 

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending