News
Kuɗaɗen sata da muka ƙwato sun kai dala biliyan ɗaya – Gwamnatin Najeriya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta gano tare da ƙwato dala biliyan ɗaya da aka sace sakamakon bincikar kuɗin sata da gwamnatin mulkin shugaba Buhari ke yi tun farkon hawansa zuwa yau.
Ministan Shari’a na ƙasar Abubakar Malami ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar shugaban ƙasar, bayan kammala taron majalisar zartarwar ƙasar da ake gudanarwa mako-mako, wanda shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya jagoranta.
Miliyoyin mutane sun yi asara yayin da gobara ta tashi a kasuwar Delta
Malami ya tabbatar da cewa ƙudin da aka ƙwato an zuba su a fannoni daban-daban na tattalin arzikin ƙasar cikin har da shiri gwamnati ƙasar na yaƙi da talauci.
Haka kuma ministan ya bayyana damuwar gwamnati kan cushe a kasafin ƙudin ƙasar, ya ce hakan abin takaici ne, ya kuma ƙara da cewa za a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki domin magance hakan.
