Connect with us

News

2023: APC ta nuna rashin amincewa da tura sakamakon zaɓe ta na’ura mai ƙwaƙwalwa

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Jam’iyyar APC mai mulki ta yi fatali da matakin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dauka na sabon tsarin tantance masu kada kuri’a (BVAS) da kuma ganin sakamakon zaɓe ta yanar gizo (IReV) inda ta ce Nijeriya ba ta kai matsayin fara amfani da irin wannan fasahar ba.

Ita dai INEC ta kafe kai da fata cewa sai ta yi amfani da wannan sabuwar fasaha a zaɓen 2023.

Advertisement

Kuɗaɗen sata da muka ƙwato sun kai dala biliyan ɗaya – Gwamnatin Najeriya

An yi ta zargin cewa jam’iyya mai mulki ta dauki nauyin yunkurin tsige Shugaban Hukumar ta INEC saboda dagewar sata amfani da na’urorin zamani don inganta harkar zabe.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ne ya bayyana haka a yammacin yau Larabaa lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar sa ido kan zabe ta ƙasashe rainon England, wadda a ka fi sani da Commonwealth.

Advertisement

Yace; “Na farko, na samu tagomashin zama sanata. Damuwarmu ita ce wanne irin shiri mu ka mu tunkari amfani da irin waɗannan fasahohin na zamani, musamman ɓangaren watsa sakamakon zaɓe. Shin za a samu nasarar watsa sakamakon zaɓe a kan lokaci?

“Don yada sakamako, kowane bangare na kasar Najeriya ban tabbata cewa hanyar sadarwa ta same shi ba, na san cewa ko da a cikin sassan Abuja akwai wuraren da babu hanyar sadarwa kuma muna da daga yanzu har zuwa Fabrairu yayin da a wasu sassan kasar nan babu wutar lantarki.

Advertisement

“Dole ne INEC ta tabbatar mana da cewa 100 bisa 100, a lokacin da za a mika sakamakon zabe sun shirya domin sun yi magana game da sake cajin batir amma mun yi zabe a baya inda ta ce ba za ta iya caji batir ba,” in ji Adamu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending