Connect with us

News

Masu gidan burodi sun fara yajin aiki a Tunisiya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

Dubban masu gidajen burodi sun fara yajin aiki a Tunisiya saboda gazawar gwamnati na biyan kuɗin tallafi cikin sama da shekara guda.

 

Advertisement

Masu gidajen burodin sun ce suna bin gwamnati bashin kusan dala miliyan 80.

FIRS tayi taron wayar da kan kungiyoye masu zaman kansu muhinmancin bayan haraji

Wannan matakin na zuwa ne bayan irin sa da masu sana’ar suka ɗauka a watan Oktoba, inda suka janye yajin aikin bayan cimma wata yarjejeniya, wadda suka ce gwamnatin ta gaza cikawa.

 

Ƙarancin burodi al’amari ne da kan iya tayar da hatsaniya a Tunisia, ƙasar da ta fuskanci jerin zanga-zanga a baya saboda ƙarancin abinci da rashin kayan more rayuwa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending