Connect with us

News

Hisbah a Kano za ta fara kama ‘yan mata da ke talla a tituna

Published

on

Ma'aikatan Hisba a bakin aiki

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

 

Advertisement

Hukumar Hisba a Kano da ke arewacin Najeriya ta fara shirin kama matan da ke talla akan titunan jihar.

Kafar yada labaran Radio Najeriya ta rawaito, mataimakiyar mukaddashin kwamanda mai kula da harkokin mata, Malama Ummulkulsum Kasim ce ta yi wannan bayanin, bayan kama wasu mata a titinan karamar hukumar Kumbotso.

Advertisement

Mata na bore kan haramcin zuwa jami’a da Taliban ta yi

Malama Ummulkulsum ta ce yawancin matan da ke talla akan tituna da daddare ‘yan mata ne da ke saida gyara da goro, da rogo, ko kayan lambu da sauransu.

Ta ce yawancin ‘yan tallan an gano su a tashoshin mota, da wurin makanikai abin takaicin kuma da daddare.

Advertisement

Malama Ummulkulsum ta ce ”hakkin iyaye ne killace ‘ya’yansu da tabbar da ba su tarbiyya da ilimi, da kare su daga aikata ba daidai ba. Kuma addinin musulunci ya tabbatar da hakan, bai kamata a bar ‘ya’ya mata da na yawo kara zube da sunan talla ba.”

Jaridar indaranka ta rawaito cewa kwanakin da suka gabata hukumar Hisba a jihar Kanon ta yi nasarar kama wasu matasa 19 kan zargin halartar auren jinsi a Kano, ko da ya ke Amarya da Angon sun tsere har yanzu ba a san inda suka buya ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending