Connect with us

News

Dan Gwamnan Nasarawa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya A. Sule, ya yi rashin dansa mai suna Hassan A. A Sule.

 

Sakataren Yada Labarai ga Gwamnan, Ibrahim Addra ne ya tabbatar da rasuwar tasa a sanarwar da ya fitar da safiyar Juma’a.

Advertisement

Zan share wa talaka hawaye kan batun sauya takardun kuɗi, in ji Kwankwaso

“A madadin iyalin Mai Girma Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule, na sanar da rasuwar dansa, Hassan A.A Sule, wanda ya rasu ranar Alhamis, 26 ga Janairu, 2023,” in ji sanarwar.

 

Marigayi Hassan ya bar duniya yana da shekara 36.

 

 

Sanarwar ta kuma bayyana cewa za a yi jana’izar marigayin a garin Gudi, cikin Karamar Hukumar Akwanga da misalin karfe 10:00 na safe a ranar Juma’a.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending