Connect with us

News

Sakataren Gwamnatin Gombe Ya Rasu Ana Saura Sati Daya Yayi Ritaya

Published

on

Babban sakataren gidan gwamnatin jihar Gombe, Balarabe Poloma,

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

A ranar Lahadi ne aka tabbatar da rasuwar babban sakataren gidan gwamnatin jihar Gombe, Balarabe Poloma,Poloma yamutu mako guda kafin ya yi ritaya daga aiki.

Advertisement

Paloma ya yi aiki da gwamnatoci daban-daban guda uku a matsayin Babban Sakatare, Gidan Gwamnatin Jihar Gombe.

Cibiyar Ciyarwa Fisabilillahi ta gudanar da rabon abinci ga marayu da masu rauni a Kano.

Paloma ya mutu yanada shekaru 60 a duniya,da yake jajantawa ’yan uwa da abokan marigayin da mazauna jihar, Gwamna Muhammadu Yahaya ya yi alhinin rasuwar PS.

Advertisement

Yahaya ya bayyana marigayin a matsayin gogaggen lauya kuma ƙwararren mai gudanar da mulki, wanda ya daɗe yana aiki da sadaukarwa, aiki tuƙuru, kwazo da kulawa da cikakken kishin jaha.

 

Advertisement

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun babban daraktan hulda da manema labarai Ismaila Misilli.

 

Advertisement

Ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayin ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi.

 

Advertisement

Barista Poloma, mai shekaru 60, ya rasu ne da sanyin safiyar yau Lahadi, 8 ga Oktoba, 2023, bayan gajeriyar rashin lafiya, kamar yadda iyalansa suka tabbatar.

 

Advertisement

Ya kamata ya yi ritaya a mako mai zuwa, domin kawo karshen doguwar hidimar wani mutum da ba kasafai ake samun taba a matsayin Babban Sakatare a gwamnatocin gwamnoni uku na jihar Gombe,” a wani bangare na sanarwar.

 

Advertisement

Yahaya ya mika ta’aziyyarsa ga matar Poloma, da sauran ‘yan uwa da suka rasu, da majalisar gargajiya ta Waja inda ya rike madafun ikon Madaki, da al’ummar karamar hukumar Balanga da ma daukacin ma’aikatan jihar Gombe.

A wani labarin kuma Cibiyar Ciyarwa Fisabilillahi ta gudanar da rabon abinci ga marayu da masu rauni a Kano.

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending