News
Cibiyar Ciyarwa Fisabilillahi ta gudanar da rabon abinci ga marayu da masu rauni a Kano.
DAGA ABDURRASHID B.IMAM
A safiyar ranar juma’a ne cibiyar mai suna ciyarwa fisabilillahi ta gudanar da rabon abinci ga marayu da masu rauni a jahar kano.
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa An gudanar da rabon ne a unguwar kawo da yakasai durumin zungura a nan jahar kano
Shugabar cibiyar khadija Ahmad yusuf wadda aka fi sani da rufaida ta bayyanawa manema labarai cewar ta fara aiwatar da wanann aiki ne a ranar 29-09-2023 ana fara da rabawa marayu hamsin dafaffan abinci haka tace gudanar da hakan ne duk domin ragewa al’umma radadin matsin rayuwa
Rufaidan ta kara da cewar wannan cibiya tana samun kudin wannan ciyarwa ne daga hannu daidaikun Al’umma masu hali
Daga karshe ta bayyana hanyar da za a same ta ga masu son taimakawa za a same ta ta lambar wayar ta kira ko whatapp 07064517451
Aminu sani da zainab zakari cikin wadan da suka samu wannan abinci sun bayyana farin cikin su hadi da godewa Allah da wannan cibiya tare da addu’ar Allah ya kara daga wannan cibiya
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News4 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
-
News21 hours ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
