Connect with us

Sports

Bayan ta kore shi shekarun baya, Chelsea ta dawo da Lampard domin farfaɗo da ƙungiyar

Published

on

Lampard

 

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Frank Lampard ya amince ya zama kocin Chelsea na rikon kwarya daga yanzu zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Advertisement

A ranar Laraba tsohon kocin kungiyar ta Chelsea ya yarda ya koma jagorancin ta shekaru sama da biyu bayan an sallame shi daga aiki.

Lampard ba shi da aiki tun bayan da aka sallame shi daga Everton a watan Janairu kasa da shekara daya da zuwansa kungiyar.

Advertisement

Real Madrid ta yi wa Barcelona dukan kawo wuka har gida ta

A watan Janairun 2021 Chelsea ta kore shi daga aiki inda ta maye gurbinsa da Thomas Tuchel.

Advertisement

Ranar Lahadi kungiyar ta kori Graham Potter daga aiki bayan shi ma ya maye gurbin Tuchel.

Chelsea na matsayi na 11 a Gasar Firimiya ta Ingila kuma ta tashi 0-0 a wasan da suka yi da Liverpool ranar Talata a Stamford Bridge.

Advertisement

Tana bayan kungiyoyi hudu da ke saman teburin Firimiya da maki 14, duk da cewa ta kashe sama da Fam miliyan 550 a bana don sayo sabbin ‘yan wasa.

TRT

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending