Connect with us

News

Najeriya na bincike kan zargin biyan miliyoyin kuɗi don yi wa ‘yan sanda ƙarin girma.

Published

on

 

 

Advertisement

Hukumar kula da aikin ‘yan sanda a Najeriya ta ce ta kafa kwamitin bincike don bin diddigin zargin cewa ana biyan sama da naira miliyan bakwai kafin a yi wa manyan jami’an ‘yan sanda ƙarin girma.

 

Advertisement

Hukumar ta yi kira ga duk wani da ke da wata shaida kan wannan zargi, ya bayyana gaban ta, don gudanar da bincike.

 

Advertisement

Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Ikechukwu Ani ya fitar ta ce matakan, martani ne kan wani rahoto da wata jaridar intanet a Najeriya ta buga mai taken ‘badaƙalar cin hanci ta tashi hankula a hukumar kula da aikin ‘yan sanda’.

Abin da ya kamata ku sani akan daren Laylatul Qadr

Rahoton ya yi zargin cewa sai an biya cin hancin $10,000, kimanin naira miliyan bakwai, kafin a yi wa manyan ‘yan sanda ƙarin girma a hukumar.

Advertisement

 

Ta dai yi alƙawarin ɗaukar mataki a kan duk jami’in da aka samu da hannu kan zargin karɓar cin hancin.

Advertisement

 

Kwamitin a cewar sanarwar Mista Ani, ya ƙunshi jami’an rundunar ‘yan sanda da kuma na hukumar kula da aikin ‘yan sanda.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending