Connect with us

Sports

Achraf Hakimi na shan yabo daga sassan duniya kan dabarar kare dukiyarsa

Published

on

 

Rabuwar auren Hiba Abouk da Achraf Hakimi dan wasan Morocco, ya bazu a kafofin yada labarai, bayan da aka ruwaito cewa matar ta shigar da kara kan dan wasan na Paris Saint-Germain da ya sake ta.

Advertisement

 

Hakimi na fuskatar tuhuma bisa zargin yi wa wata mata fyade, lokacin da matarsa tare da yaransu da kuma mahaifiyarsa suka yi balagurio zuwa Dubai.

Advertisement

EFCC Ta Baza Jami’anta guda100 A Kano

Mujallar First Mag ta Faransa ta ruwaito cewa Hiba na neman rabin kadarorin da Hakimi ya mallaka, amma ta yi mamaki da ta samu labarin cewa ba shi da komai a sunansa.

 

Advertisement

Hakan na nufin Abouk ba za ta karbi wani bangare na dukiyar tsohon mijin na ta ba

 

Advertisement

Wanda ke cin gajiyar albashi da dukiyar Hakimi ba kowa ba ne illa mahaifiyarsa wadda ta shafe shekaru da dama tana karbar albashin sa a asusun bankinta.

 

Advertisement

Duk da cewa wannan labari ya ya janyo hankali sosai a kasashen Spain Faransa da kuma Moroko, duk kuwa da cewa Abouk ba ta cikin wani hali da take bukatar wani bangare na dukiyar tsohon mijin nata domin samun damar taimaka wa rayuwa, la’akari da cewa itama tana da tata dukiyar, amma abin mamakin shine yadda ta nemi a bata rabin dukiyar dan wasan.

 

Advertisement

Al’umma da dama daga sassan duniya, na jinjina wa dan wasan, musamman yadda ya nuna kauna ga mahaifiyarsa, da kuma kaucewa fada wa irin wannan sarkakiya, la’akari da yadda matan ‘yan kwallo da dama kan nemi makudan kudade idan suka nemi rabuwa da su.

 

Advertisement

Sai dai a wasu wuraren kuma, dan wasan ya sha suka, inda wasu ke ganin bai kamata ya mika ragamar dukiyar tasa kacokan ga asusun mahaifiyar tasa ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending