Connect with us

News

Hukumomin Saudiyya sun kama wani ɗan Najeriya ɗaya da ‘yan Saudiyya uku bisa zargin safarar hodar ibilis

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Hukumomin Saudiyya sun kama wani ɗan Najeriya ɗaya da ‘yan Saudiyya uku bisa zargin safarar hodar ibilis da ta kai nauyin kilogiram 2.2 a ƙasar.

Advertisement

Sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan ƙasar ya ce ya samu nasarar daƙile yunƙurin shigar da hodar ibilis zuwa biranen Riyadh da Jeddah.

Yazama wajibi Tinubu Ya Aiyana Kadarorin Da Ya Mallaka Kafin Ranar 29 Ga Watan Mayu.

‘Yan sandan sun ce mutanen huɗu sun daɗe suna aikata laifin safarar hodar ibilis ɗin tare da sayar da ita a cikin ƙasar ta hanyar amfani da wasu miyagun dabaru.

Advertisement

Jami’an ‘yan sandan sun ce za a gurfanar da mutanen a gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike.

Safarar ƙwaya dai babban laifi ne a Saudiyya da za a iya yanke wa mutum hukuncin ɗaurin shekaru masu yawa a gidan yari

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending