News
Ɗaurarru dubu 75,507 na cinye abincin naira biliyan 22.44 duk shekara a gidajen yari — Jami’i
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin tarayya na kashe Naira biliyan 22.44 a shekarar ɗaya wajen ciyar da fursunoni 75,507 a gidajen gyaran hali a fadin kasar, in ji wani jami’i a yau Alhamis a Abuja.
Babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Dr Shuaib Belgore ya bayyana cewa fursunonin sun bazu a cibiyoyin gyaran hali 244 a fadin kasar.
Belgore ya ce kashi 70 na fursunonin ma su jiran shari’a ne
Ya kuma danganta yawan fursunonin da ke jiran shari’a da kamasu ba bisa ka’ida ba, da tsaiko wajen tabbatar da adalci da kuma kasa cika sharuddan beli.
Sakataren ya ce hakan ne ya janyo cunkoso a gidajen yari guda 82 a fadin kasar.
Advertisements
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
