News
Shugabar Kwamitin Afuwa Ta Kano Ta Bukaci Al’umma Su Taimakawa Daurarru
Shugabar Kwamitin Yi Wa Daurarru Afuwa a Jihar Kano, Hajiya Azumi Namadi Bebeji, ta yi kira ga al’umma, musamman masu hali, da su taimaka wa mutanen da ke gidajen gyaran hali domin rage masu damuwa da yanayin da suka tsinci kansu a ciki.
Ta bayyana hakan ne yayin da take mika shanu 12, shinkafa da kayan miya ga daurarru a madadin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, domin su samu damar yin shagalin bikin Sallah Karamar.
Hajiya Azumi ta jaddada cewa taimakon da aka kai ya dace da lokaci, domin daurarru su samu damar jin daɗin Sallah kamar sauran al’umma. Ta kuma bayyana cewa hakan zai ƙarfafa su da kuma ba su kwarin gwiwar ganin canji a rayuwarsu.
A nasa bangaren, mai magana da yawun gidajen gyaran hali na Kano, CSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya nuna godiya ga gwamnatin jihar bisa wannan tallafi.
Shugabar kwamitin, Hajiya Azumi, ta samu rakiyar wasu daga cikin mambobin kwamitin yayin mika tallafin.
