Connect with us

News

Dalibai masu rijista ne kawai suka cancanci zama don zana jarrabawa– KSP

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Hukumar gudanarwar kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kano ta sanar da ranar Lahadi 14 ga watan Mayu, 2023 a matsayin ranar rufe aikin rijista sannan kuma ranar 15 ga watan Mayun 2023 za a fara fara jarabawar zango na 1 da 3.

Advertisement

Shugaban makarantar, Dakta Kabir Bello Dungurawa ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai kai tsaye bayan taron manyan jami’an hukumar da aka gudanar a ranar Laraba 10 ga watan Mayu, 2023.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa za a rufe aikin rajistar wanda ya dauki kusan watanni biyar ana rufe shi a ranar Lahadi da tsakar dare kuma daliban da suka kammala rajista da buga katunan jarabawa ne kadai za a ba su damar zuwa wuraren da za a yi jarrabawar.

Advertisement

Ya kuma shawarci daliban da ba su kammala rajista ba da su yi hakan kafin ranar rufewa.

Ya kuma yi nuni da cewa, za a ci gaba da yin rijistar daliban na wucin gadi saboda za a sanar da ranar rufe ta daga baya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending