News
Za a fara yi wa maniyyata gwaje-gwajen lafiya a Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta sanar da cewa A Yau za ta fara aikin yi wa maniyyatan aikin hajjin bana gwaje-gwajen lafiya.
Mataimakiyar daraktan wayar da kai da ilimintarwa ta hukumar, Hadiza Abbas Sanusi ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar.
SHUGABANCIN MAJALISAR DATTAWA: Sai na ga abinda ya ture wa buzu naɗi – Yari.
Ta ce za a gudanar da gwajin lafiyar a cibiyoyin kiwon lafiyar jihar daga ranar Litinin, 14 ga Mayu.Ta sanar da cewa kowane mahajjaci ya karbi fom din gwajin lafiyarsa daga jami’in aikin Hajji a kananan hukumominsu inda su ka biya kudin aikin Hajjin.
Advertisements
