News
Mutum 17 Ne Suka Mutu Akan Gadar Jirgin Kasa Da Ta Karye
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI.
Akalla mutum 17 ne suka mutu akan gadar jirgin kasa da aka gina lokacin da gadar ta karye a yau laraba a yankin gabashin Mizoram yayin da wasu da dama suka bace.
Rahotanni na nuni da cewa Ministan yankin ne ya dora bidiyon yadda gadar ta karye a shafukan sada zumunta.
Nyesom Wike ya yi alƙawarin kammala aikin jirgin ƙasan Abuja nan da wata shida
Gwamnatin kasar dai tayi alkawarin biyan diyyar Dala bilyan biyu da dubu dari hudu ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su.
Mizoram na da nisa tsakanin gabashin Indiya inda take da iyaka da Myanmar.