News
Mutum 12 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Nasarawa
DAGA AISHA MUHAMMAD.
Majalisar Nasarawa ta aike sakon ta’aziya ga gwamnatin jihar da karamar hukumar Lafia kan mutuwar mutane 12 a hadarin jirgin ruwa a kogin Kungra da ke Arikiya ta karamar hukumar Lafia.
Kakakin majalisar, Mista Ibrahim Balarabe Abdullahi, wanda ya shaida hakan a wani zaman gaggawa ya aike sakon ta’aziya ga iyalan mamatan da suka hada da mata da maza.
Jirgin dauke da mutum 19, akwai 7 da suka tsira.
Karamar hukumar Lafia da sauran yankunan kasar sun shiga zaman makoki.