News
Rugujewar Gini: Tinubu da Wike Sun Shiga Ganawar Sirri a Abuja
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike a ranar Alhamis, sun shuga wata ganawar sirri a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Taron ya zo ne a daidai lokacin da ginin ya ruguje wanda ya faru da sanyin safiyar ranar Alhamis
Toshewar Magudanar Ruwa Ta zama Babbar Barazana A Jahar Kano
Ba a bayyana ajandar taron ba amma watakila bai rasa nasaba da rugujewar ginin da ta afku a Abuja a ranar Larabar da ta gabata, inda ake fargabar mutuwar mutane kusan biyu tare da jikkata wasu 37.
Ana sa ran Ministan zai yi wa shugaban kasa bayani kan lamarin da ya faru da kuma irin asarar da aka samu.
Advertisements
