News
Toshewar Magudanar Ruwa Ta zama Babbar Barazana A Jahar Kano
DAGA ISAH MAGAJI RIJIYA BIYU
Toshewar Magudanar ruwa a wasu sassan a jihar Kano ya zama Babbar barazana ga al, ummar jihar kano.
Jaridar Indaranka ta rawaito cewa Indan akayi duba da yanayin Damuna da muke ciki hakan ka iya janyo ambaliyar ruwa kamar yadda yasha faruwa a baya.
Gwamnatin Jahar Kano Zata Rabawa Mata Awaki Domin Dogaro Da Kai
Ko a shekarar data gabata sai da aka samu mummunar ambaliyar ruwa a Jihar Kano da Jigawa wanda hakan ya janyo mutuwar mutane da dama.
Su daga cikin wadanda Jaridar Indaranka tatauna da sun baiyana cewa Toshewar Magudanar ruwa ta zama babbar matsala ga rayuwar su.
Hukumar KARMA wadda itace keda alhakin lura da Toshewar Magudanar ruwa a jihar Kano tace gwamnati tana iya kokarinta ganin an samu gyara akan matslaar kuma akwai ayyukan da ake gudanarwa a kowacce hanya da kuma tituna dake Kano.