News
Wani mutum dan shekara 35 ya rataye kansa saboda tsadar rayuwa a Jigawa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Wani magidanci mai suna Samaila Ilu mai shekaru 35 ya rataye kansa har lahira sakamakon mawuyacin halin da yake ciki a jihar Jigawa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar wa da jaridar DAILY POST faruwar lamarin.
Mutane 6,000 sun tsere daga muhallinsu sakamakon ambaliyar ruwa a Jihar Neja
A cewarsa, “A ranar 17/08/2023 da misalin karfe 11:00 na safe ‘yan sanda sun samu rahoton cewa wani matashi mai suna Samaila Ilu mai shekaru 35 a kauyen Dungun Tantama a karamar hukumar Hausa ya bar gidansa.
Ya ce daga baya an tsinci gawarsa rataye akan bishiya da igiya, ana zaton ya kashe kansa ne.
Shiisu ya ce, tawagar ‘yan sanda sun kwashe gawar tare da kai shi asibiti domin a duba gawar.
Ya ce tun daga lokacin aka mika shi ga ‘yan uwansa domin yi masa jana’iza.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
