News
Mace Ta Rasu, Wasu Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gadar Sa’i
Wata mata ta rasa ranta, wasu kuma da dama sun jikkata a wani hatsarin mota da ya afku a gadar Sa’i da ke kauyen Matari, Karamar Hukumar Soba a Jihar Kaduna.
Shaidu sun ce hatsarin ya faru ne sakamakon lalacewar gadar, wadda ke haddasa irin wadannan hadurra lokaci zuwa lokaci.
Matar Aure Ta Aikata Kisan Kishiyarta A Gaban Mijinta A Katsina
Al’ummar yankin sun sha rokon gwamnati da ta kawo dauki domin gyaran gadar, amma har yanzu ba su samu mafita ba.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun shaida wa Arewa Updates cewa sun dade suna gudanar da aikin gayya don gyara gadar, amma gyaran ba ya dadewa saboda yawan ababen hawa da ke wucewa ta wajen.
Wannan ba shi ne karo na farko da hatsari ke faruwa a kan gadar ba.
Advertisements
