Sports
Taiwo Awoniyi Na Cikin Masu Takarar Gwarzan Dan Wasan Premier Na Watan August

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Dan wasan Super Eagles, Taiwo Awoniyi ya kasance cikin jerin sunayen ‘yan wasanda da aka zaba domin takarar gwarzon dan wasan Premier na watan Agustan bana.
Dan wasan na kungiyar kwallon kafa ta Nottigham Forest ya zira kwallaye uku a wasanni hudu da ya buga wa Forest, wanda ya kara nuna bajintarsa ta iya tamaula.
Sanarwar da aka fitar a jiya, ta baiyana cewar an zabi ‘yan wasa shida domin takarar kanbun gwarzon dan wasan na watan Augusta.
Dan wasa Awoniyi ya tsawaita yawan zura kwallo a raga tun daga kakar wasan da ta gabata zuwa wasanni bakwai a jere a gasar Premier, wanda shi ne dan wasan Afrika na uku da ya yi hakan.
Wani labarin kuma Mutane 30 Sun Mutu A Wurin Hakar Ma’adinai Dake Abuja
Gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu ya dawo gida Najeriya bayan dogon hutun da ya dauka domin duba lafiyarsa a kasar Jamus.
Gwamnan ya bar Najeriya watanni ukku da suka gabata domin duba lafiyarsa a kasar ta Jamus.
Shugaban masu rinjaye a zauren majalisar dokokin jihar Ondo, Wole Ogunmolasuyi, wanda ya tabbatar da dawowar gwamnan ga wakilinmu, Ya ce a yanzu haka gwamnan yana gidansa dake birnin Badun.
Kazalika maid akin gwamnan, Uwargida Betty ta tabbatar da dawowar mai gidan nata a shafinta na X, inda ta wallafa hotonsa a cikin jirgin sama.