Connect with us

Sports

Shin Da Gaske Ne Ahmad Musa Ya Fice Daga Tawagar ‘Yan Wasan Nijeriya  

Published

on

Kyaftin tawagar kwallon kafa ta Nijeriya, (Super Eagles), Ahmed Musa

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Kyaftin tawagar kwallon kafa ta Nijeriya, (Super Eagles), Ahmed Musa, ya karyata rade-radin cewa ya fice daga tawagar ‘yan wasan Nijeriya bayan shafe tsawon lokaci ba tare da ya bayyana a gaban ƴan jarida ba.

Advertisement

Leadership ta ruwaito cewa a wata tattaunawa da ya yi da ‘yan jarida a Kaduna ranar Juma’a bayan kammala wasan sada zumunta da ya shirya wa matasan Arewacin Nijeriya,ya ce batun ficewarsa daga tawagar Super Eagles ba wani abu bane face jita-jita.

Rana Irin Ta Yau M. K. O. Abiola Ya Rasu A Ranar Da Za A Sake Shi

Na dan tafi hutu ne kawai daga tawagar ta Najeriya, amma ban fice ba ina fatan zuwa gaba kaɗan zan dawo domin ci gaba da taimakawa Nijeriya wajen ganin ta lashe manyan kofuna. Cewar Ahmad Musa.

Advertisement

Ya kuma ce yana fatan wannan bayanin nasa zai canza tunanin da dama daga cikin magoya bayansa da ke tunanin cewa ya dakata da bugawa tawagar Super Eagles kwallo.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending