Connect with us

Sports

An dakatar da Paul Pogba kan zargin shan kayan kara kuzari

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

An dakatar da dan wasan Juventus da Faransa Paul Pogba daga kwallon kafa bayan an gano yana shan abubuwan kara kuzari.

“Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta sanar a yau Litinin, 11 ga watan Satumba, 2023, cewa Paul Labile Pogba ya karbi takardar dakatarwa daga kotun yaki da shan kayan kara kuzari bayan gwajin da aka yi masa ranar 20 ga watan Agusta,” in ji kungiyar.

Advertisement

An Yi Holin Kwamishinan ‘Yan Sandan Bogi, da Wasu Mutane 12

“Kungiyar tana da damar yin nazari kan mataki na gaba,” a cewar sanarwar.

An dakatar da Pogba ne bayan Juventus ta doke Udinese ranar 20 ga watan Agusta a wasan da aka bar shi a benci.

Advertisement

Pogba, wanda ya lashe Kofin Duniya a 2018, shi ne dan wasa mafi tsada lokacin da ya bar Juventus zuwa Manchester United a 2016. United ta biya €105m ($116.4m) domin sayen Pogba daga Juventus.

Ya taimaka wa Manchester United wajen cin Kofin UEFA Europa na 2017.

Advertisement

A 2022, Pogba ya sake komawa Juventus amma ba kasafai yake buga wasa ba sakamakon raunukan da yake fama da su.

A wani labarin kuma An Yi Holin Kwamishinan ‘Yan Sandan Bogi, da Wasu Mutane 12

Advertisement

Gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu ya dawo gida Najeriya bayan dogon hutun da ya dauka domin duba lafiyarsa a kasar Jamus.

Gwamnan ya bar Najeriya watanni ukku da suka gabata domin duba lafiyarsa a kasar ta Jamus.

Advertisement

Shugaban masu rinjaye a zauren majalisar dokokin jihar Ondo, Wole Ogunmolasuyi, wanda ya tabbatar da dawowar gwamnan ga wakilinmu, Ya ce a yanzu haka gwamnan yana gidansa dake birnin Badun.

Kazalika maid akin gwamnan, Uwargida Betty ta tabbatar da dawowar mai gidan nata a shafinta na X, inda ta wallafa hotonsa a cikin jirgin sama.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending