Connect with us

Sports

Kano Pillars Ta ‘Dauki Kofin Share Fage Na Hadin Kan Kungiyoyin Arewa

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta zama zakara a Gasar Cin Kofin zaman Lafiya da hadin kan kungiyoyin Arewa domin share faggen shiga kakar wasanni ta bana da aka yi a Kano.

Gasar ta mako guda an fafata tsakanin kungiyoyi hudu da suka hada da, Kano Pillars da Gombe United da Katsina United da kuma kungiyoyin kwallon kafa na Neja Tornadoes.

Advertisement

Ana fargaba fiye da mutum 20,000 sun mutu a bala’in ambaliyar Libya

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta zama zakara da maki bakwai a wasanni uku da ta buga, inda ta ci wasa biyu da canjaras daya.

Mai horas da ‘yan wasan sai masu gida, Abdu mai Kaba, yace akwai sauran aiki a gaban kungiyar kuma sun gano kura-kurai da za’a dauki matakan gyara.

Advertisement

Da yake sanar da rufe gasar a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar mata Kano da yammacin jiya Laraba, shugaban kwamitin wasanni na majalisar dokokin jihar Kano Alhaji Kabiru Dahiru ya taya kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars murna tare da bayyana wasan kwallon kafa a matsayin wani abu na hada kan al’ummar kasarnan.

Wani labarin kuma Ana fargaba fiye da mutum 20,000 sun mutu a bala’in ambaliyar Libya

Advertisement

 

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

Advertisement

 

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

Advertisement

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending