Sports
Rashford Ya Yi Hatsarin Mota A Hanyarsa Ta Zuwa Gida
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rashford Ya Yi Hatsarin Mota A Hanyarsa Ta Zuwa Gida Bayan Tashi Daga Wasansu Da Burnley
Tauraron dan kwallon Manchester United, Marcus Rashford, ya yi hatsarin mota yayin da yake tafiya gida bayan da kungiyarsa ta doke Burnley da ci 1-0 a ranar Asabar.
Rashford, mai shekaru 25, an ba da rahoton cewa Rashford ya yi karo da wata motar yayin da yake barin filin atisaye na United Carrington.
Rashford ya buga wasa da Burnley, amma ya kasa jefa kwallo a raga a wasan da kyaftin din kungiyar Bruno Fernandes ya jefa kwallo daya tilo a wasan.
Rahotanni sun ce ‘yan sanda sun isa wurin inda suka kai daukin gaggawa.
Wata majiya ta ce Rashford ya girgiza amma bai ji rauni ba.
Bruno Fernandes, wanda ya zura kwallo daya tilo a Turf Moor, ya zo kan wurin da lamarin ya faru kuma an yi imanin ya tsaya don ba da taimako.