Sports
NPFL ta tsayar da ranar da za’a fara gasar League din Najeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar kula da gasar League ta kasa ta ce kungiyoyi 20 da za su fafata a gasar ta bana za su sami naira miliyan 10 kowaccensu, bayan da ta sanar da ranar 30 ga watan da muke ciki na Satumba a matsayin ranar da za a fara gasar, biyo bayan dage ta har sau biyu.
Wannan na zuwa ne bayan da aka kara yawan kudaden da za a bai wa kungiyar da ta lashe gasar daga naira miliyan 100 zuwa naira miliyan 150.
Ta cikin wata takarda da hukumar ta aikewa kungiyoyin mai dauke da sa hannun shugaban gudanarwarta Davidson Owumi, ta ce hukumar ta yi iya bakin kokarin ta wajen magance matsalolin da za su sa a sake dage fara gasar.
Sanarwar ta ce tana bukatar kungiyoyin cikin gaggawa su aike da lambobin asusun ajiyar bankinsu da za a sanya musu kudaden kafin lokacin da za a fara buga wasanni.
NPFL ta ce nan gaba kadan za ta fitar da tsarin jadawalin yadda gasar za ta kasance da kuma yadda za a rinka yada ta kai tsaye a shafin hukumar.
Wani labarin kuma Hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano zai ruguje kamar dodo a kotun daukaka kara—Kperoogi
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro
