News
Za Mu Tsayar Da Komai Cak A Najeriya Ranar 3 Ga Watan Oktoba – ’Yan Kwadago NLC
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar ta ce za ta tsayar da komai cak a fadin Najeriya.
Ƙungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun amince su fara yajin aikin sai baba-ta-gani a duk fadin Najeriya daga ranar 3 ga watan Oktoba.
Kungiyoyin kwadago sun sanar da shiga yajin aikin sai baba-ta-gani
Kungiyoyin sun umarci dukkan mambobinsu da rassansu a fadin Najeriya da su tsayar da komai cak a fadin daga ranar Talatar mai zuwa.
Shugabannin kungiyoyin, Joe Ajaero na NLC da Festus Osifo na TUC ne suka bayyana hakan ga manema labarai jim kadan da kammala wani taronsu na gaggawa a sakatariyar ’yan kwadago ta kasa da ke Abuja ranar Talata.
Sun ce za su tsunduma yajin aikin ne saboda Gwamnatin Tarayya ta gaza cika musu alkawuran da ta yi musu domin rage raɗaɗin janye tallafin man fetur.
’Yan kwadagon sun ce za a ci gaba da yajin aikin ne har sai abin da hali ya yi.
A baya dai ƙungiyoyin sun ba gwamnatin wa’adin kwana 21 domin ta biya musu bukatun, amma wa’adin ya cika a makon da ya gabata ba tare da cim ma wata matsaya ba.
Ko a farkon watan Satumbar nan sai da kungiyoyin suka yi yajin aikin gargadi na kwana biyu, sannan suka ce a shirye suke su wuce ma har sai abin da hali ya yi zuwa karshen watan.
Daga cikin bukatun nasu har da na karin albashi da kuma na rage wasu haraji da ma’aikatan Najeriya ke biya domin su rage radadin.
Wani labarin kuma Kungiyoyin kwadago sun sanar da shiga yajin aikin sai baba-ta-gani
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro