Connect with us

Business

Ƴan Najeriya sun kashe N2.6tn wajen sayen katin waya da data a cikin watanni 9

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Masu amfani da layukan sadarwa a Najeriya sun kashe kusan naira tiriliyan 2.6 wajen siyan katin waya da na data a cikin watanni tara na farkon shekarar 2023, kamar yadda kamfanonin sadarwa na MTN Nigeria da Airtel Africa suka fitar.

Advertisement

Hakan ya nuna an samu karuwar kashi 32.57 cikin 100 daga naira tiriliyan 1.95 da aka samu a shekarar 2022.

An Kone Sama Da Tan 15 Na Miyagun Kwayoyi A Jihar Kano

A ɓangaren kamfanin sadarwa na Airtel, ya ce abubuwan da ke haifar da wannan shi ne ƙaruwar masu siyan data da kuma faɗuwar darajar naira

Advertisement

A cikin watanni tara na farkon shekarar 2022, Airtel ya samu dala biliyan 1.41 daga siyan katin waya da kuma data wanda lokacin da aka canza shi akan farashin N461 kan dalar Amurka ɗaya da aka samu a lokacin, ya kai naira biliyan 647.71.

A daidai wannan lokacin na 2023, kuɗaɗen shiga da waɗannan kamfanonin biyu suka samu a ɓangaren siyan katin waya da data sun kai dala biliyan 1.29 wanda lokacin da aka canza shi akan farashin naira 777 kan dala ɗaya ya kai naira tiriliyan 1.003.

Advertisement

A ɓangaren MTN, ƙaruwar masu siyan katin waya da data ne ke ƙara haɓaka da kuma kawowa kamfanin ci gaba.

Bbc ta ruwaito cewa Kuɗaɗen siyan data sun ƙaru da kashi 36.36 cikin 100 duk shekara, yayin da kuɗaɗen katin waya ya ƙaru da kashi 10.64 cikin 100, wanda ke nuna ƙaruwar amfani da Intanet a faɗin ƙasar.

Advertisement

A wani labarin kuma An Kone Sama Da Tan 15 Na Miyagun Kwayoyi A Jihar Kano

An saki Falasdinawa 33 da ake tsare da su a gidajen kason Isra’ila da tsakar daren jiya, yayin kuma da tun da fari Hamas ta saki Isra’ilawa 11 da suka haɗa da ‘yan asalin Jamus da Argentina da Faransa.

Advertisement

Shugaban jam’iyyar Palestinian National Initiative, a yamma da Gabar kogin Jordan, Moustapha Barghoti yace dakatar da buɗe wuta ce kadai abinda ya dace.

Ya ce a halin yanzu kofa a bude ta ke ta cimma tsagaita wuta baki daya, wannan shi ne abin da duniya baki daya ke so.

Advertisement

Bayan wannan ya kamata a sako dukkan Isra’ilawan da ake tsare da su da Falasdinawa, wannan shi zai kawo zaman lafiya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending