Connect with us

News

Angola Da Najeriya Sunki Amincewa Da Bukatar Kungiyar OPEC Na Rage Yawan Man Da Suke Hakowa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Najeriya da Angola sun ki amincewa da matakin da kungiyar kasashe masu arzikin fitar da man fetur ta duniya Opec ta bukaci su dauka, na rage yawan man da suke hakowa.

Rahotonni sun bayyana cewa, kawancen Kasashen da Saudiyya ke jagoranta ba su samu cimma matsaya ba da Angola da Najeriya, wadanda suka nuna rashin amincewarsu da rage yawan man da suke hakowa.

Advertisement

Dan Sandan Ya Harbi Mutane A Cikin Keke NAPEP A Jihar Kaduna

Wani wakili a yayin ganawar ya ce ba lallai ba ne a iya cimma matsaya a tsakanin bangarorin biyu kafin taron da kungiyar ta OPEC da za’a yi a gobe 30 ga Nuwambar 2023.

A wani labarin kuma Dan Sandan Ya Harbi Mutane A Cikin Keke NAPEP A Jihar Kaduna

Advertisement

Ƴan ci-ranin Moroko hudu sun mutu a gaɓar tekun kudancin Sifaniya, kusa da birnin Cadiz, inda aka kai wasu huɗu zuwa asibiti saboda tsananin sanyi.

An gano gawawwakin mutanen huɗu waɗanda suka nutse a ranar Laraba a cikin kwale-kwalen da ya ɗauki ƴan ci-rani 32.

Advertisement

An ruwaito cewa ma’aikatan jirgin sun tilastawa 27 daga cikin mutanen tsalle zuwa cikin tekun, kuma an ceto 23 da rai.

Ƴan sandan Sifaniya sun fara bincike kan lamarin.

Advertisement

Mataimakiyar Firaiministar Sifaniya kuma ministar kwadago, Yolanda Diaz, ta ce “ta firgita” da labarin.

“Abu ne mara daɗi yayin da waɗanda suka zo neman rayuwa mai inganci suka gamu da ajalinsu,” in ji ta, yayin da take kira ga Turai ta ɗauki mataki.

Advertisement

Ƙasar Sifaniya dai na ɗaya daga cikin manyan wuraren da ƴan ci-rani ke tashi daga Arewacin Afirka zuwa Turai, inda a cikin shekarar da ta gabata kaɗai, dubbunai suka tsallaka cikin Turai.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending