News
Mutane 16 Sun Rasu, Wasu 30 Sun Samu Rauna A Hatsarin Tirela A Jos
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Mutane 16 sun rasu, wasu 30 sun samu rauna a hatsarin babbar mota a yankin Jos da ke Jihar Filato.
Wata tirela makare da kaya da mutane ce ta yi adungure ta fada a wani rami, inda mutum 11 suka rasu nan take, wasu kimanin 30 suna samu raunuka.
Aminiya ta ruwaito cewa Kwamndan Hukumar Kiae Haddura a Kasa (FRSC) a jihar Filato, Alphonsus Halim Godwinya ce, “karin wasu 5 sun rasu daga bisani a asibiti.”
Jami’in ya bayyana cewa motar ta fito ne daga Jihar Kano za ta Abuja, lokacin da ta samu hatsarin aHauwan-Kibo da ke Karamar Hukumar ta Jos Kudu.
Alphonsusya ce wasu daga cikin wadanda suka samu raunin an kai su asibitin sojoji, wadanda suka samu rauni mai tsanani kuma an kai su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUH).
Ya ce hatsarinya auku ne sakamakon tsinkewar burkin motar wadda ke dauke buhunan hatsi.
Da haka ta roki matafiya da su guji neman saukin kudin mota sa ya sa aloda su a cikin motocin daukar kaya
A wani labarin kuma Wani Mutum Ya Halaka Kansa Ta Hanyar Rataya A Jihar Adamawa
Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar
Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar.
Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.
Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara.
Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.
Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.
Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.
