Connect with us

News

Kuɗaɗenku ba sa fuskantar haɗari a banki – CBN

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Babban bankin Najeriya, CBN ya bai wa ƴan ƙasar tabbaci cewa kuɗaɗen ajiyarsu da ke asusun bankuna ba sa fuskantar wani haɗari inda ya jaddada samun daidaito a tsarin bankunan ƙasar.

Babban bankin ƙasar ya shawarci jama’a da su ci gaba da haulɗa da bankuna kamar yadda aka saba inda ya nemi ƴan ƙasar su yi watsi da rahotanni marasa tushe game da halin da bankunan ƙasar ke ciki.

Gwamnan Ondo, Akeredolu ya rasu Yana da shekaru 67 a duniya.

Bbc ta ruwaito cewa CBN ya ce yana da dukkan kayan aikin da ake buƙata wajen gudanar da ayyukansa da suka shafi hada-hadar kuɗaɗe.

Wata sanarwa da mai riƙon muƙamin sashen yaɗa labarai na CBN, Hakama Sidi-Ali ta fitar, ta ce “Babban bankin CBN ya ga wasu rahotanni a wasu kafafen yaɗa labarai game da shawarar da aka bai wa gwamnatin tarayya na karɓe iko da wasu cibiyoyin kuɗi ƙarƙashin kulawarsa.

“Bankunan Najeriya suna harkokinsu yadda ya kamata. CBN na shawartar jama’a su ci gaba da tafiyar da harkokinsu ba tare da samun fargaba kan rahotannin da ake yaɗawa ba waɗanda ba daga CBN suka fito ba.” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending