News
Shehu Sani ga gwamnoni: Ku dena ɗiban kuɗin talakawa ku na kai wa Tinubu gaisuwa a jiragen haya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya yi kira ga gwamnonin Najeriya da su daina barnatar da kudaden jama’a wajen ɗaukar jiragen haya domin kai gaisuwa ga shugaba Bola Tinubu.
Ya kuma roki shugaban kasar da ya hana gwamnoni barin jihohinsu a lokutan bukukuwa saboda kalubalen tsaro da ake fuskanta.
Fiye da mutum 20 sun mutu sakamakon fashewar bututun ɗanyen mai a jihar Ribas
Sani, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani a kan ziyarar da kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, ‘su ka kaiwa Tinubu a gidansa da ke Legas a jiya Talata, ya koka da cewa hakan na da illa ga tattalin arziki da tsaro ga gwamnatocin jihohi.
A wani sako da ya wallafa a sashihin shafin sa na X a jiya Talata, Sani ya ce irin wadannan ziyarce-ziyarcen na kara wa jihohi nauyi mai yawa na kudi, yana mai jaddada cewa ya kamata shugabannin Najeriya su yi da gaske wajen rage kudin gudanar da mulki.
“Bayan wadannan bukukuwan, ya kamata shugaban kasa ya hana gwamnonin jihohi barin jihohinsu don kai masa gaisuwa.
“Na farko, babban nauyi ne a kan kudaden jihohi. Farashin jirage masu haya da sauran kuɗaɗe.
“Na biyu kuma, da alama ana samun ci gaba da fuskantar barazanar tsaro a lokutan bukukuwan.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
