Connect with us

News

Shugaba Tinubu ya buƙaci hafsoshin tsaron Najeriya su kakkaɓe matsalar rashin tsaro a ƙasar

Published

on

DAGA IBRAHIM BELLO SALE 

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bukaci shugabannin tsaron ƙasar da su tabbatar da ɗaura ɗamara domin magance matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta.

Advertisement

Yayin da yake jawabi ga manyan hafsoshin tsaron a taron majalisar tsaron ƙasar da ya gudana a fadar gwamnatinsa ranar Juma’a da maraice , shugaban Tinubu ya ce yayin da ake samun ci gaba a kakkabe matsalolin tsaro da ƙasar ke fama da su, akwai buƙatar ƙara jajircewa don tabbatar da magance matsalolin tsaron da ke ci wa ƙasar tuwo a ƙwarya.

Kisan Filato: Wasu Mata Masu Zanga-Zanga Sun Kone Gidan Wani Basaraken Gargajiya

“Nasarar da kuke samu abin a yaba ne. ‘Yan Najeriya na gani a ƙasa, amma ya kamata a yi ƙoƙarin kauce wa kura-kurai, irin wanda aka gani a baya-bayan nan a jihar Kaduna, haƙiƙa haɗin kai da ake samu takanin jami’an tsaro na ƙara inganta a watannin baya-bayan nan, amma a yanzu ba lokacin nuna murna ba ne, har sai mun kakkaɓe matsalar baki ɗayanta,” in ji shugaba Tinubu.

Advertisement

Bbc hausa ta ruwaito cewa Shugaban ya kuma ya buƙaci sojojin da su tabbatar da muradin ƙasar na haƙo ganga miliyan biyu na man fetur a kowace rana a cikin rubu’in farko na shekarar 2024.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending