Connect with us

Sports

Afcon 2023: Nigeria Ta Chasa Ivery Coast Masu Masaukin Baki A Wasan Hamayya

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Najeriya ta lallasa masu masaukin baki yayin arangamar da aka yi a filin wasa na Alassane Ouattara.

Advertisement

Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta samu nasarar doke kasar Ivory Coast a Gasar Kofin Afirka ta AFCON 2023 da suka fafata a Yammacin ranar Alhamis a Abidjan.

Gwamnatin Tarayya za ta fara bai wa ɗalibai lamuni – Ministan Ilmi

Super Eagles wadda ta samu nasarar farko a gasar wadda aka soma a wannan makon, ta yi wa Ivory Coast wadda ita ce mai masaukin bakin ci daya mai ban haushi yayin aragamar da aka yi a filin wasa na Alassane Outtara da ke birnin Abidjan.

Advertisement

Kwallo daya ce ta raba gardamar da aka kwashe minti 90 ana yi, inda kyaftin din Super Eagles, William Troost-Ekong ya kankaro wa ’yan Najeriya martaba a bugun daga kai sai mai tsaron raga da ya jefa a minti na 54.

Wannan shan kashi da tawagar ta Ivory Coast ta yi ita ce rashin nasara ta farko da aka samu wata kasa mai masaukin baki ta yi a wasannin rukuni tun bayan wadda Equatorial Guinea ta yi a shekarar 2012 lokacin da ta yi hadakar saukar baki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending