Connect with us

Sports

Dalilin da ya sa AS Roma ta zabga wa Jose Mourinho takardar sallama

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Jose Mourinho ya fuskanci sallamarsa ta shida, a wannan karon da kungiyar kwallon kafa na AS Roma bayan kusan shekaru uku a kungiyar.

Sanarwar da AS Roma ta fitar ta ce” Aiki tsakanin ta da Mourinho ya kare kwatakwata.

Sai Kun Yi Haƙuri, Amma Sai Gwamnati Ta Ɗauki Matakai Masu Tsauri – Buhari

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Muna so mu gode wa José a madadin mu duka a AS Roma saboda da kokarinsa tun zuwansa kulob din,” in ji Dan da Ryan Friedkin.

Muna yi wa José da mataimakansa fatan alheri a ayyukansu na gaba.”

Advertisement

Wannan shi ne karo na shida da kociyan mai shekaru 60 ke barin kulob, inda a baya ya fice daga Chelsea a 2007 da 2015, Real Madrid a 2013, Manchester United a 2018, da Tottenham a 2021.

An bayyana shi a matsayin kocin kungiyar na 60 a watan Mayun 2021, zaman Mourinho a Roma ya hada da lashe gasar League a kakar wasa ta 2021/22 da kaiwa wasan karshe na gasar Europa a Budapest a watan Mayun da ya gabata.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending