News
Gwamnatin Jihar Jigawa Za Ta Gina Ajujuwan Makarantun Islamiyya Guda 132 A Faɗin Jihar.
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gwamnatin Jihar Jigawa Za Ta Gina Ajujuwan Makarantun Islamiyya Guda 132 A Faɗin Jihar.
Hakan na ƙunshe cikin batutuwan da Majalisar Zartaswar Jihar ta amince da su, a taron ta na ranar Laraba.
Ma’aikatar Kula da Ilmi a Matakin Farko ce ta gabatar wa majalisar tsare-tsaren buƙatar gina ajujuwan, waɗanda kuma aka amince za a kashe Naira Miliyan Ɗari Biyar da Talatin da Biyu, da Dubu Ɗari Huɗu da Saba’in da Ɗari Tara da Saba’in da Bakwai (N532,427,977.58) wajen aikin ginin.
Ginin wanda za a yi a garuruwa daban-daban a mazaɓu 30, zai ƙunshi gine-gine 66 a faɗin jihar, wanda kowane na ɗauke da ajujuwa biyu.
Shirin dai ya na ƙunshe ne cikin ayyukan mazaɓu da gwamnati za ta yi a cikin 2024.
Haka kuma a taron na Majalisar Zartaswa, kamar yadda sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai, Sagir Musa Ahmed ya sa wa hannu, ta amince shawarwarin da kwamiti kan Babbar Kwalejin Fasaha ta Bilyaminu Usman da ke Haɗejia ya gabatar.
Premium Times ta ruwaito cewa akan haka Majalisar Zartaswa ta amince a aiwatar da shawarwarin a cikin gaggawa.
Sannan kuma an amince da kafa kwamitin mutum biyar kan manyan makarantu huɗu na jihar da suka haɗa da Babbar Kwalejin Ilmi Mai Zurfi ta Gumel, Matakarantar Koyon Shari’a da Addinin Musulunci ta Ringim, Babbar Kwalejin Fasaha ta Bilyaminu Usman da kuma Babbar Kwalejin Fasaha ta Dutse na tsawon shekara ɗaya.
