Connect with us

News

Dalilan mu na shiga zawarcin ‘yan kwankwasiyya da jagoransu- Ganduje

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta shiga zawarcin kananan jam’iyyun adawa ciki harda NNPP ta Rabi’u Musa Kwanwkaso da mabiyansa.

Advertisement

Shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya shaida wa BBC cewa tuni suka aike da goron gayyata ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da jagoran jam’iyyar NNPP na kasa Rabiu Musa Kwankwaso.

AFCON 2023: Me ya sa ’yan Nijeriya ke son Onana ya kama gola a wasan da za su yi da Kamaru?

Ganduje ya yi waɗannan kalamai ne a wani taro da ya jagoranta da shugabannin jam’iyyarsa ta APC a jihar Kano, inda ya ce dama can uwa ɗaya uba ɗaya suke da su Kwankwason.

Advertisement

A cewa Ganduje, “Wannan ya zama dole saboda a matsayina na shugaban jam’iyyar APC na kasa ina zagayawa jihohi, sanatoci sun shigo cikin wannan jam’iyya tamu ‘yan majalisar tarayya sun shigo wannan jam’iyya tamu, haka nan kuma gwamnoni.

Shugaban APC ya ce nan gaba ma akwai wadanda za su shigo cikin jam’iyyar, kuma wannan dalili ne ya sa ya fito yana neman hadin kai daga jiharsa ta Kano.

Advertisement

“Na ma kira wasu na waje ballantana namu na gida” in ji shi.

Sai dai shugaban jam’iyyar APC ya ce kawo yanzu ba su rubutawa jagoran jam’’iyyar NNPP da gwamnan jihar Kano wasika a hukumance ba game da wannan kiran da suka yi mu su.

Advertisement

A cewarsa suna son ɓangaren Kwankwaso ya nuna sha’awar shiga jam’iyyarsu ta APC kafin a je matakin aike wasika.

Wannan bukata ta APC na zuwa ne adaidai lokacin da jama’a da dama ke nuna shaku kan ba lallai tafiyar tayi kyau ba tsakanin Kwankwaso da Ganduje a inuwa guda.

Advertisement

Amma Ganduje ya nuna kwarin gwiwa tare da tunasar da cewa, “ai dama can gidanmu ɗaya, dama can Ubanmu ɗaya, an samu rarrabuwar kai, yanzu kuma idan Allah ya sake haɗawa, to me ya fi wannan daɗi”.

A KWARARO MUKA TSINCI LABARIN – NNPP

Advertisement

Sai dai jam’iyyar hamayya ta NNPP a Kano ta ce kawo yanzu babu wanda ya tuntubeta game da shiga jam’iyyar APC.

Sanusi Bature Dawakin Tofa mai magana da yawun gwamna Abba Kabir Yusuf, ya shaidawa BBC cewa wannan kira da shugaban APC ya yi musu a kwararo suka ji shi.

Advertisement

”Mun ji bayyanin cewa ya miko wannan ƙoƙon bara na gwamna ya dawo jam’iyyar APC to amma abin mamaki shi ne, shi Ganduje a matsayinsa na tsohon gwamna da tsohon mataimakin gwamna ya fi kowa sanin hanyar da ake isarwa gwamna mai ci sako idan ana son ya je wurinsa”, in ji Sanusi.

Ya kuma kara cewa gwamna Yusuf ba shi da wata matsaya ta barin jam’iyyarsa ko kin barin jam’iyyarsa.

Advertisement

”Amma maganar da muka ji ya faɗa a kafafen yaɗa labarai na zumunta mu ka ji ta kuma a nan mu ka barta’’

”Ka san ita siyasa ko in ce sauya sheka ta siyasa kamar canza gida ne, ba ka tashi lokaci ɗaya kawai ka dauki jakarka ka fita, ka ce wai ka canja gida.

Advertisement

“Akwai abubuwan da za ka iya yi kafin ka ce ka canja gida saboda don haka mu a wurinmu wannan sako mun ji ne kawai kamar a sama”, in ji shi.

Wannan yunkuri na jam’iyyar APC na zuwa ne bayan umarni da shugaba Tinubu ya bayar, na cewa ɓangarorin biyu su je su sasanta da juna.

Advertisement

Wasu dai na ganin cewa abu ne mai matuƙar wuya waɗannan ɓangarori su iya ajiye rigingimun da ke tsakaninsu su yi aiki tare idan ta tabbata cewa za su haɗe, musamman kan wanda zai zama jagora.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending