News
Kashi 50 Bisa 100 Na Magungunan Da Ake Shigo Da Su Najeriya Duk Jabu Ne Kuma Masu Haɗarin Gaske – Hukumar NAFDAC
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Hukumar Kiyaye Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta yi kakkausan gargaɗi tare da yin kururuwar a yi hattara, dangane da ambaliyar magungunan jabu a cikin Najeriya daga ƙasashen waje.
Shugabar Hukumar NAFDAC, Mojisola Adeyeye ce ta bayyana haka ranar Litinin, a lokacin taron masu ruwa da tsaki kan harkokin NAFDAC, ciki har da jami’an tsaro.
Zanga-Zangar Da Mata Suka Gudanar A Minnna Akan Tsadar Kayan Abinci Ta Razana Shugaba Tinubu
Ta ce a yanzu fice da kashi 50 bisa 100 na magungunan da ake shigowa da su cikin ƙasar nan, duk jabu ne, ba su da inganci, ba su da takardar shaidar sahihancin rashin haɗarin su ga lafiyar jama’a, kuma su na da illa a jikin masu amfani da su.
Mafi abin buƙata wajen ingancin magani dai a taƙaice shi ne ya kasance ya cika dukkan sharuɗɗan da Hukumar Lafiya ta Duniya ta shimfiɗa.
Adeyeye ta ce magunguna marasa inganci kuma na jabu su na kawo babbar barazana ga lafiyar jama’a, sannan su na gurgunan ta damar samuwar ingantattun magunguna ga marasa lafiya. Haka kuma su na haifar da cikas wajen kaiwa ga nasarar samar da kiwon lafiya a ƙasar nan da ma Afrika baki ɗaya.
Ta ce “Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin ta gindiya sharuɗɗa cikar ingancin magunguna (CPP), waɗanda NAFDAC ke aikawa ƙasashe, tare da umarnin cewa sai magungunan da suka cika waɗannan sharuɗɗa za a shigo da su Najeriya.
Premium Times ta ruwaito cewa Adeyeye ta ce yawancin magungunan da ake shigowa da su Najeriya, duk ana sayo su ne da ƙasashen Kudu maso Gabas Nahiyar Asiya.
Ta ce bisa bin tafarkin Hukumar Lafiya ta Duniya, Najeriya ta hana shigo da wasu magunguna da dangogin su har daban-daban har kala 140.
