Connect with us

News

Raɗaɗin Tsadar Rayuwa Ya Harzuƙa Ƙungiyoyin Ƙwadago, Sun Bai Wa Gwamnati Wa’adin Shiga Yajin Aiki 

Published

on

DAGA MUHAMMAD BASHIR MUSA

 

Advertisement

Manyan ƙungiyoyin ƙwadago biyu na Najeriya, wato NLC da TUC, sun bai wa Gwamnatin Tarayya kwanaki 14 ta fara aiki da tsare-tsaren da ta yi alƙawari tun a cikin watan Oktoba, domin ta sauƙaƙe wa ‘yan Najeriya matsanancin halin ƙuncin rayuwar da ake ciki.

Tuni dai jama’a ke ta ƙorafin tsadar rayuwa da ake fama da ita, tun bayan cire tallafin fetur.

Advertisement

Ma’aikatar Lafiya Ta Jihar Kano Da OHAI Sun Kulla Yarjejeniya Kan Tiyatar Lebe 

Karya darajar Naira da Gwamnatin Tinubu ya yi ya haifar da masifaffiyar tsadar kayan abinci da kayan masarufi da sauran tsadar ayyukan yau da kullum.

Cikin wata sanarwar da NLC da TUC suka fitar bai-ɗaya, sun bayyana damuwar su dangane da “yadda Gwamnatin Tarayya ta ƙi fara aiki da sharuɗɗa 16 da ke cikin yarjejeniyar da ta cimma da ƙungiyoyin ƙwadagon a ranar 2 ga Oktoba, 2023.”

Advertisement

“Waɗannan yarjejeniyar da aka cimma da gwamnatin tarayya sun bada fifiko ne wajen samar da sauƙin rayuwa ga talaka da sauran jama’a, waɗanda ke jin jiki, bayan Bankin Duniya da IMF sun yi wa Najeriya ingiza mai kantu ruwa, ta cire tallafin fetur da kuma karya darajar Naira.” Cewar NLC.

Dangane da hakan ne NLC da TUC suka ce sun fahimci babu makawa sai dai kawai su bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin makonni biyu, tun daga gobe Juma’a, 9 ga Fabrairu, 2024.”

Advertisement

Jaridar Inda Ranka ta buga labarin yadda zanga-zangar mata a Minna, babban birnin Jihar Neja ta kai mata sun fito kan titi su na zanga-zangar nuna damuwa dangane da tsadar kayan abinci da masarufi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending