News
DMCSA Ta Kaddamar da Kwamitin cikin Gida Kan inganta Sashen Sarrafa Magunguna
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
A shirinsa na daukar matakin gaggawa kan tabbatar da ci gaba a kan lokaci a Hukumar Samar da Magunguna ta Jiha (DMCSA), Darakta Janar na Hukumar, Pharm. Gali Sule ya kaddamar da wani kwamiti na cikin gida wanda zai yi nazari kan shawarwarin da kwamitin inganta sashen sarrafa magunguna (DMU) na hukumar ya bayar.
A makon da ya gabata ne Kwamishinan Lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya karbi rahoton kwamitin inganta sashin sarrafa magunguna na DMCSA da Farfesa Bashir Chedi ya jagoranta.
Sai da aka sace ni na fara goyon bayan biyan kuɗin fansa – Tsohon daraktan DSS
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwar da Jami’in Yada Labarai na Ma’aikatar Lafiya Ibrahim Abdullahi ya turawa da Jaridar Inda Ranka.
Da yake magana, Pharm. Gali Sule ya ce an kafa kwamitin na cikin gida ne musamman don duba shawarwarin da kwamitin da ya gabata ya bayar don yiwuwar aiwatar da su a matakin hukumar, yana mai amincewa da cewa wasu shawarwarin sun wuce hukumar ta aiwatar sai a matakin ma’aikatar lafiya, yayin da wasu kuma aiwatar da su sai a mataki mafi girma na gwamnatin jiha.
Darakta Janar din ya bayyana cewa, bunkasa samar da magunguna a cikin gida ta hanyar inganta DMU na daga cikin ajandar mai girma Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a lokacin da aka zabe shi a karagar mulki, hasali ma hakan na daga cikin alkawurran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe da yake cikawa cikin nasara.
Pharm. Gali ya jaddada cewa DMU shi ne sashi mafi muhimmanci a DMCSA duk da cewa ayyukan da sashin ke gudanarwa sun yi kadan, don haka akwai matukar bukatar inganta sashin ta yadda zai yi aiki yadda ya kamata.
“Akwai ƙofofi da damammaki da dama da ke zuwa, idan muka rasa su tabbas za mu rasa damammakin da ke zuwa jihar.
“Ma’aikatar lafiya ta tarayya tana da wani shiri a bana don tallafa wa jihohin da ke da sassan sarrafa magunguna masu inganci. ba ma son a bar jihar Kano a baya,” in ji Darakta Janar.
Ya yi nuni da cewa, ana bukatar inganta sashin ne domin cibiya ce da jami’o’i da sauran manyan makarantun gaba da sakandare ke turo dalibansu domin samun horo, ya kara da cewa hatta Kwalejin Babbar Difloma ta Horar da Dalibai kan Harhada Magunguna ta Afirka ta Yamma na turo dalibanta domin horar da su a sashin, don haka akwai bukatar sake nazari da inganta matsayin sashin.
Daga nan sai Pharm. Gali ya bukaci mambobin kwamitin da su yi aiki tuƙuru a kan aikin da aka ba su domin an zaɓe su ne bisa cancanta da kuma tarihin da suke da shi na hidimta wa al’umma.
Ya kuma yi kira gare su da su dauki wannan aiki a matsayin wani bangare na yi wa bil’adama hidima kamar yadda Hukumar ke son daidaita ayyukanta, ya kuma bukace su da su lura da cewa daya daga cikin ayyukan hukumar ta DMCSA shi ne samo ko sarrafa magunguna masu inganci da araha da hakan ba zai yiwu ba ba tare da samun ingantaccen sashin sarrafa magunguna ba.
Da yake mayar da jawabi, shugaban kwamitin, Pharm. Nasir Jibril Rikadawa, ya jinjina wa Pharm. Gali saboda nasarorin da cimma a cikin kankanin lokaci da ya sake farfado da ayyukan hukumar.
Ya ba da tabbacin aniyarsu ta yin aiki ba tare da gajiyawa ba bisa ga ka’idojin da aka ba su a wani yunkuri na ba da tasu gudummawar wajen inganta sashin don cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Pharm. Usman Saminu, Pharm. Nafisa M. Bashir, Pharm. Abdulaziz Hamisu da Pharm. Fatima S. Abdullahi.
Sauran sun hada da Kabiru Musa Gwarzo, Zainab Ismail Zakariyya, Maryam Abdulkadir, PT Mahmud Umbara da kuma Dahiru Ibrahim Malami wanda zai zama Sakatare.