News
Dalilin da ya sa EFCC ke cigiya da farautar matar Emefiele, sirikin sa da wasu mutum biyu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Watanni shida bayan cire tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele da kuma damƙe shi, Hukumar EFCC na farautar matar sa, surikin sa da wasu mutum biyu bisa zargin harƙalla, damfara da almundahana.
Waɗanda ake cigiyar sun haɗa da Margaret Emefiele, matar Godwin Emefiele, sai Jonathan Omoile, matar sa Anita, ‘yar uwa da kuma wani mutum ɗaya wanda jami’in Babban Bankin Najeriya (CBN) ne, mai suna Eric Odoh.
Kwaddebuwa Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirka Bayan Ta Ci Najeriya 2-1
Haka dai EFCC ta bayyana a shafin ta na Tiwita, wato X a ranar Asabar.
Eric Ocheme Odoh, Margaret Dumbiri Emefiele, Anita Joy Omoile da Jonathan Omoile duk EFCC ta buga gangar cigiya da farautar su.
Tuni dama Godwin Emefiele da matar sa su na fuskantar tuhuma a Babbar Kotun Abuja, dangane da zarge-zargen harƙallar satar biliyoyin kuɗaɗe.
Waɗanda ake cigiyar a yanzu dai EFCC ta ce sun haɗa baki da Emefiele suka sace maƙudan kuɗaɗe mallakar Gwamnatin Tarayya.
Sannan kuma an zarge su da aikata laifin cin amanar ƙasa da zamba, musamman laifukan da suka saɓa da Sashe na 411, 287 da 314 na Dokar Laifin Zamba ta Jihar Legas.
Sanarwar ta roƙi jama’a duk wanda ya san inda suke ko wani daga cikin su ya ɓoye, to ya tuntuɓi Ofishin EFCC, ko kuma ya buga lambar wa 08093322644.
EFCC ta ce Odoh ɗan asalin Jihar Benuwai ne, kuma ganin ƙarshe da aka yi masa shi ne a Ofishin CBN da ke Garki, kuma ana kyautata zaton ma’aikacin bankin ne.
Ita kuma matar Emefiele ‘yar asalin Jihar Delta ce kuma Shugabar Kamfanin Harkokin Mai na Dummies Oil & Gas Ltd.
Rabon da a ji ɗuriyar ta tun wani gani da aka yi mata a gidan ta a Legas, mai Lamba 38 kan titin Iru Close, Ikoyi.