Connect with us

News

Har yanzu ‘Yan kasuwar Chanji na wapa suna hannun jami,an hukumar EFCC

Published

on

Yan kasuwar chanji na wapa

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

 

A safiyar jiya Laraba ne jami’an Hukumar EFCC suka yi dirar mikiya a kasuwar WAPA a wani yunkuri na yaki da ayyukan masu boye Dala.

Advertisement

 

Hukumar EFCC ta tsare wasu ’yan kasuwa a samamen da jami’anta suka kai kasuwar ’yan canji ta WAPA da ke Jihar Kano a ranar Laraba.

Advertisement

 

Wani ganau mai suna Malam Isma’ila Zico, ya ce jami’an na EFCC “Sun nuna kwarewa, sai daga bisani muka gano cewa tun safe suke nan.

Advertisement

 

“Lokacin da za su fara aikin ne sai muka ga masu jaket dinsu sun shigo, suka yi wa wajen yan canji kawanya.

Advertisement

Jaridar bustandaily ta rawaito cewa ba,a,san ko mutum nawa suka kama ba, amma dai sun tafi da wasu ’yan canjin,” in ji Zico, wanda ya ce an kai samemen ne a yayin da ake tsaka da hadahadar kasuwanci.

 

Advertisement

EFCC ta kai samemen ne a yayin da ake tsaka da hadahadar kasuwanci, suka yi awon gaba da wasu daga cikin yan kasuwar

 

Advertisement

Shugaban yan canji na kasuwar, Alhaji Sani Salisu Dada, ya tabbatar da kamen ne wanda ya ce za a binciki wadanda aka yi awon gaban da su na.

 

Advertisement

Amma ya kara da cewa an ci gaba da harkoki yadda aka saba a kasuwar, kuma a shirye suke su ba da hadin kai ga hukuma.

 

Advertisement

A ceawrsa, jami’an EFCC sun kai samamen ne domin shawo kan matsalar masu boye dala da kuma ’yan canji masara lasisi.

 

Advertisement

Hakan na zuwa ne sakamakon ci gaba da tashin gwauron zabo da dalar ke yi a wurin ’yan canji a sassan kasar, inda farashin dalar ya kai N1,900.

 

Advertisement

A ranar talata gwamnatin tarayya ta umarci hukumomin tsaro da su dauki matakin kamawa, bincike da kuma hukunta masu wannan dabi’a.

 

Advertisement

Ko a ranar talata jami’an EFCC sun kai makamancin wannan samame a kasuwar ‘yan canji da ke unguwar Zone 4 da ke Abuja.

 

Advertisement

A safiyar Laraba ma rahotanni sun nuna cewa an kai irin wannan samame a kasuwar ’yan canji da ke Unguwar Sabo a garin Ibadan, Jihar Oyo.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending