Sports
An Dakatar Da Cristiano Ronaldo Daga Buga Wasa Saboda ‘Rashin Ɗa’a’
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
An dakarar da Cristiano Ronaldo daga buga wasa ɗaya saboda samunsa da laifin rashin ɗa’a a fafatawar da Al Nassr ta doke Al Shabab da ci 3-2, in ji Kwamitin Yaƙi da Rashin Ɗa’a na Hukumar Kula da Ƙwallon Ƙafar Saudiyya (SAFF) ranar Laraba.
Bidiyoyin da aka riƙa watsawa a soshiyal midiya sun nuna yadda ɗan wasan na Portugal ya toshe kunnuwansa sannan ya riƙa saka hannayensa a kusa da mazakutarsa, a wani mataki da ake gani tamkar cin-fuska ne ga magoya bayan ƙungiyar da suka fafata da ita.
Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Kano ta dakatar da nadin Hakimi a Bichi
Kazalika kwamitin ya ce dole ne Ronaldo ya biya tarar riyal 10,000 ($2,666) ga Hukumar Kula da Ƙwallon Ƙafar Saudiyya, da kuma riyal 20,000 ($5,332) ga ƙungiyar Al-Shabab bisa ƙorafin da ta shigar. Sai dai yana iya ɗaukaka ƙara.
Ɗan ƙwallon wanda sau biyar yana lashe kyautar Ballon d’Or ya tafi Al-Nassr daga Manchester United a bara, kuma tun daga wancan lokacin ne wasu manyan ƴan wasa suka bi sawunsa inda suka tafi ƙungiyoyin ƙwallon kafar Saudiyya.