News
Mutum 12 Sun Mutu, 28 Sun Jikkata A Wani Hadarin Mota A Hanyar zariya Zuwa Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Mista Kabir Nadabo, Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) na jihar Kaduna, ya ce akalla mutane 12 ne suka mutu sannan 28 suka samu raunuka a wani hadarin mota da ya rutsa da su a hanyar Zariya zuwa Kano.
Nadabo ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai Na Kasa NAN a ranar Litinin a Kaduna cewa, hatsarin motan ya yi sanadiyar rayuka a kauyen Tashar Yari da karfe 7:36 na safiyar ranar Litinin.
Nikki Haley ta kayar da Trump a zaben fitar da gwani a Washington
“Tirelar mai lamba KTG 454 ZZ tana kan hanyar zuwa Kano lokacin da lamarin ya faru,” in ji Nadabo.
Ya ce abin da ya haddasa hatsarin ya faru ne bisa kuskure,da Kuma wuce gona da iri .
Ya ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa mutane 40 ne suka samu hatsarin, 28 sun samu raunuka, 12 kuma sun mutu.
Daily News24 ta ruwaito cewa An kai wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Makarfi domin ci gaba da kula da su.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
