News
Ku mayar wa ‘yan kasuwa kayan abinci da kuka ƙwace, umarnin Tinubu ga Hukumar Kwastom
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban Hukumar Kwastam, Bashir Adeniyi ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umarci hukumar ta mayar da duka abincin da ta ƙwace daga wajen mutane a iyakokin Najeriya domin siyar da su a kasuwannin kasar nan.
Cikin wata sanarwa da hukumar Kwastam ɗin ta fitar a shafinta na X, ta ce Adeniyi ya bayyana hakan ne lokacin wata ziyara da ya kai iyakar Kwangwalam da ke ƙaramar hukumar Mai’adua a jihar Katsina inda ya gana da masu ruwa da tsaki ranar Asabar.
Adeniyi ya ce Tinubu ya yi haka domin kawo sauki ga al’ummar Najeriya duk da cewa doka ta bada dama a kwace kayan kuma kada a maida wa masu fasakwuari kayansu.
Ya ce za a saka ido a tabbatar an dawo da abincin cikin gida kuma an siyar da su ga al’umman Najeriya cikin sauki.
Idan ba a manta ba, Jami’an kwastam sun kama motocin kaya sama da 22 a makon jiya cike makil da buhunan kayan abincin za a fice kasar nan da su.
Sai dai kuma Tinubu ya umarci da a maida wa masu shi da dukka waɗanda aka kama a baya, amma fa da sharaɗin ,a su saida su a kasuwannin Najeriya.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
