News
Azumi: Hukumar Tace Fina-finai Ta Bada Umarnin Kulle Gidajen Galar Dake Fadin Jahar Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar tace Fina-finai da Dab’i ta jahar Kano ta bada umarnin kulle dukkannin gidajen Galar dake fadin jahar Kano.
Wannan na zuwa ne biyo bayan wata ganawa da Shugaban Hukumar yayi da jagororin yan Kungiyar ta musu gidajen galar reshen jahar Kano a ofishin sa.
KWASTAM: “Ku maida wa mutane abincin su da ku ka kwace a iyakokin Najeriya —Shugaba Tinubu
A cewar shugaban Hukumar Abba El-mustapha, dokar zata fara aiki ne tun daga yau lahadi har zuwa 1 ga watan shawwal wato ranar bikin karamar sallah.
Abba El-mustapha ya gargadi masu gidajen wasannin na gala da su guji Karya doka domin duk wanda Hukumar ta samu da laifin karya wannan dokar to hakika zata dauki tsastsauran mataki a kansa wanda ka iya sawa ya rasa lasisin sa na din-din-din
El-mustapha ya kuma godewa jagorori tare da yan Kungiyar ta masu gidajen gala hadi da al’ummar jahar Kano dangane da hadin kan da suke bawa Hukumar a kowanne lokaci.
A karshe ya Kara tunatar da dukkannin al’umma cewa kofar sa’ a bude take domin bashi shawara ko sanar da Hukumar duk wani al’amari da zai taimake ta domin samun nasarar aiyukan data saka a gaba .
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
