Connect with us

News

Yanzu-Yanzu: An Ga Watan Ramadan A Saudiyya

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Rahotanni daga Kasar Saudiyya sun tabbatar da ganin jinjirin watan azumin Ramadan na bana a sassa daban-daban na kasar a ranar Lahadi.

Hakan dai na nufin ranar Litinin ce, za ta kasance daya ga watan Ramadan na shekarar 1445 bayan Hijira, wacce ta yi daidai da 11 ga watan Maris 2024.

Azumi: Hukumar Tace Fina-finai Ta Bada Umarnin Kulle Gidajen Galar Dake Fadin Jahar Kano

Hakan na zuwa ne bayan watan Sha’aban ya cika kwana 29, inda dama watannin Musulunci ba sa wuce kwana 29 zuwa 30.

Al’ummar Musulmai a fadin duniya dai kan azumci tsawon Ramadan, wanda shi ne wata na tara a kalandar Musulunci, inda suke kauracewa ci da sha da kuma saduwa da iyali tun daga fitowar rana har zuwa faduwarta.

Advertisement

Kazalika, azumi na daya daga cikin shika-shikan addinin Musulunci guda biyar.

A halin yanzu dai a Najeriya ana jiran dakon sanarwa daga Fadar Sarkin Musulumi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, game da ganin watan na Ramadan.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending