Connect with us

News

Gwamnatin Tarraya Ta Tallafa Wa Maniyyatan Hajjin Bana Da Biliyan 90

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fitar da zunzurutun naira biliyan 90 domin tallafa wa maniyyatan hajjin bana, inda ta mika kudin ga gwamnatin Saudiya kamar Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya ta bankado.

Jaridar ta ce, wata kwakkwarar majiya daga Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ce ta sanar da ita wannan labarin a ranar Alhamis.

Advertisement

CBN Ya Yi Wa Bankuna Ƙarin Jarin Da Za Su Mallaka zuwa Naira biliyan 500. 

Majiyar wadda ba a bayyana sunanta ba, ta ce, ba don tallafin na gwamnatin Najeriyar ba, da an bukaci kowanne maniyyaci da ya biya karin naira miliyan 3.5 kan kudin da ya fara biya na naira miliyan 4.9.

Kazalika wani babban jami’i a fadar shugaban kasa ya gasgata wa Daily Trust matakin tallafin na gwamnatin tarayya.

Wannan na zuwa ne a yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da cece-kuce kan yadda aka tsauwala farashin kujerar hajjin bana, abin da suka ce ba a taba ganin irinsa a tarihin kasar.

Advertisement

Hukumar Alhazan ta Najeriya ta sanar da karin kusan naira miliyan 2 sakamakon zubewar darajar kudin naira, lamarin da ya tilasta wa wasu maniyyata yanke shawarar hakura da zuwa aikin hajjin a bana, suna masu cewa, kudin ya fi karfinsu.

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya ta sanar da karin kudin kujerar hajji

Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya ta sanar da karin naira miliyan 1 da dubu dari tara da dubu 18 kan kudaden aikin hajjin da aka biya a baya, inda ta sanya ranar 28 ga watan da muke ciki na Maris matsayin ranar karshe da maniyyata zasu cika kudin.

Advertisement

Wannan bayani na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar Fatima Sanda Usara.

Fatima ta ce wannan ya zama wajibi la’akari da yadda darajar nairar Najeriya ke zubewa a kowacce rana.

Mahajjata na gudanar da tawafi a Ka’aba dake Makkah na kasar Saudiya.

Advertisement

Mahajjata na gudanar da tawafi a Ka’aba dake Makkah na kasar Saudiya. AP – Amr Nabil

Hukumar ta bukaci maniyyatan da ke son sauke farali a bana kuma suka riga da bayar da kudin ajiya, su gaggauta cika kudin daga yanzu zuwa 28 ga Maris din nan.

 

Advertisement

Gwamnan Kano ya yi wa maniyyata hajjin bana ragin kudi

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta rage wa dukkanin maniyyatan hajjin bana naira dubu 500 kan kowacce kujera biyo bayan karin da Hukumar Alhazan Najeriya ta yi har kusan naira miliyan 2.

Gwamnan ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook a wannan Larabar a daidai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce kan yadda aka tsauwala farashin kujerar hajjin a bana.

Advertisement

Sakamakon karin kudi har kimanin Naira miliyan daya da dubu dari tara (1,900,000) da Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya ta yi akan kowacce kujerar aikin Hajji, ina farin cikin sanar da dukkanin maniyyatan jihar Kano cewar Gwamnatin Kano ta musu ragin Naira dubu dari biyar (500,000) akan kowacce kujera. Inji Gwamnan Kano

Sanarwar ta kara da cewa ” Wannan ragi da muka samar a yanzu haka na nufin duk wani maniyyaci da ya biya naira miliyan hudu da dubu dari bakwai (4,700,000) kudin babbar kujera da wadanda suka biya naira miliyan hudu da dubu dari biyar (4,5000,000) kudin karamar kujera za sucika Naira miliyan daya da dubu dari hudu (1,400,000) ne kacal maimakon Naira miliyan daya da dubu dari tara (1,900,000).

Sai dai tuni ‘yan Najeriya musamman mazauna yankin arewacin kasar suka fara tsokaci kan matakin na gwamnan Kano, inda wasu ke yin san-barka, yayin da wasu ke cewa, bai kamata gwamnan ya dauki nauyin biya wa duk wani maniyyaci naira dubu 500 ba, ganin irin halin matsin rayuwa da ake fama da shi a kasar.

Advertisement

 

 

FRI

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *